fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Real Madrid ta huce haushi a kan Osasuna da ci 4-1

Real Madrid ta je ta doke Osauna da ci 4-1 a wasan mako na 23 a gasar cin kofin Laliga da suka fafata ranar Lahadi.

Osasuna ce ta fara cin kwallo minti 14 da fara wasa ta hannun Unai Garcia.
Sai dai kuma Real ta farke ta hannun Francisco Alarcon Suarez wanda ake kira Isco, sannan kyaftin Sergio Ramos ya kara na biyu.
Saura minti shida a tashi daga wasan Lucas Vazquez ya ci wa Real kwallo na uku, sannan Luka Jovic ya karkare da na hudu daf da alkalin zai tashi gumurzun.
A ranar Alhamis ne Real Sociedad ta fitar da Real daga Copa del Rey na bana, bayan da ta yi nasara da ci 4-3 a wasan da suka yi Santiago Bernabeu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wannan nasarar da Real ta yi ranar Lahadi a La Liga ta ci gaba da jan ragamar teburi da maki 52 kenan bayan wasan mako na 23.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Babban Bishop na Cocin Omega Ministry (OPM), Apostle Chibuzor Chinyere dake Fatakwal ya yi tayin mayar da iyayen marigayiya Deborah Samuel zuwa Fatakwal

Sai da dare ne Barcelona wadda take biye da Madrid da maki 46 za ta kece raini a gidan Real Betis wato Estadio Benito Villamarin.

Real Madrid za ta buga wasan mako na 24 a gasar cin kofin La Liga ranar 16 ga watan Fabrairu da Celta Vigo a Santiago Bernabeu.

Daga nan ne Real za ta ziyarci Levante a gasar La Liga ranar 22 ga watan Fabrairu, sannan ta karbi bakuncin Manchester City a Champions League ranar 26 ga watan Fabrairu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.