Saturday, July 20
Shadow

Rigakafin ciwon hanta

Hanta na da matukar muhimmanci a jikin mutum wadda ke taimakawa gudanarwar jiki sosai dan haka yana da kyau mutum ya kula da lafiyarta.

Akwai hanyoyi da yawa da mutum zai yi amfani dasu dan kula da hantarsa ta yanda in Allah ya yarda, ba zata kamu da ciwo ba.

Hanyoyin sune:

Motsa Jiki: Motsa jiki na da matukar muhimmanci wajan sa hantar mutum ta kasance cikin lafiya da aiki yanda ya kamata.

Ka a sha ko a daina shan Giya: Shan giya na taimakawa wajan lalata hantar mutum, dan haka idan ana sha sai a daina, idan kuma ba’a sha, sai a kiyaye kada a sha.

Karanta Wannan  Maganin ciwon hanta

A kiyayi shan magungunan gargajiya: Yawan shan magungunan gargajiya barkatai, yana iya kaiwa ga mutum ya sha abinda zai illata hantarsa, dan haka a daina sha zai fi ko a kiyaye.

Shan Coffee: Masana sun ce shan Coffee yana taimakawa lafiyar hanta.

Cin Abinci me gina Jiki: Kiyayewa da cin abinci me gina jiki zai taimakawa hantarka ta rika aiki yanda ya kamata.

A daina yin hadin gambizar magunguna barkatai ana sha ba tare da umarnin likita ba, wasu magungunan idan aka hadasu da wanda basu dace ba suna iya illata hanta, dan haka a tuntubi likita kamin shan magani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *