fbpx
Monday, June 27
Shadow

Rikici Ya Kaure Tsakanin ‘Yan Boko Haram Da ISWAP

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Rikicin ya barke tsakanin Boko Haram da ISWAP wanda ya yi sanadin kashe babban kwamandan Boko Haram, Ummate Ma, da wasu yan ta’addan da dama.

Rahotanni sun nuna cewa ISWAP ta kai wa tawagar Ummate Ma hari ne a Dutsen Mandara ta bude masa wuta ta kuma kwace makamai da babura dake hannun mutanan sa.

Bayanai na sirri suna nuna cewa ISWAP ta kai wa tawagar Ummate Ma harin ne a matsayin martani kan kashe kwamandansu Abou Sadiqou tare da tawagar sa.

Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa mummunan rikici ya kaure tsakanin kungiyar ta’addanci ta ISWAP da ta Boko Haram, wacce ta yi sanadin kashe hatsabibin kwamanda mai suna Ummate Ma, da wasu mutanan sa.

An tattaro cewa Ummate Ma, wanda aka fi sani da Muhamma wanda ke da mukamin Khayd (Gwamna) da mayakansa, an kashe su ne a ranar 1 ga watan Yuni lokacin da mayakan ISWAP suka kai wa tawagar Kwamandan hari a Dutsen Mandara a karamar hukumar Gwoza a hanyarsa ta zuwa Kamaru.

Karanta wannan  kalli hoton matar data ce 'yan sanda sunci zakinta a ofishinsu na jihar Osun

A cewar bayanan sirri da Zagazola Makama, Kwararre kan tsaro da yaki da ta’addanci a Tafkin Chadi ya samu daga majiyar sojoji, wacce Leadership ta samu, harin ya yi sanadin musayar wuta na tsawon awa biyu tare da kashe yan Boko Haram da dama.

Majiyar ta ce: “Yan ta’addan ISWAP din da suka taso daga kauyukan Cinana Gwoshe, Barawa da Agaba a motocci da babura sun ci galaba kan yan Boko Haram, suka kashe da dama cikinsu tare da kwace makamansu, babura da motocci masu bindiga.

Majiyar ta ce an harbi kwamandan da bindiga a kirjinsa da wasu sassan jikinsa.

Muna rokon ubangiji Allah ya azurta kasar mu Nijeriya da zaman lafiya mai daurewa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.