Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar na fuskantar barazana kan samun goyon bayan ‘yan jam’iyyar sa na PDP.
Bayan wannan kuma akwai sauran rikice-rikice dake cike da jam’iyyar inda aka samu rahotanni masu cewa an kori shugaban jam’iyyar, Iyorchia Ayu, amma dai jam’iyyar ta musanta hakan.
Saidai gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom yace sun baiwa Atiku shawarar ya dauki Wike a matsayin mataimakinsa amma ya kiya.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV inda yace shima dai bai yanke shawarar ko zai goyi bayan Atikun ba ko kuwa a’a.
The current President of Nigeria is a 2-term Northern Presidency, thus implying that it MUST be a Southern Presidency in 2023 or NOTHING. Awa ‘South’ lo kan’. Nigerians should await details soon.
— Peter Ayodele Fayose (@GovAyoFayose) June 29, 2022
Hakanan kuma wasu daga kudancin Najariya da suka hada da Fayose da sun bayyana cewa basu san da maganar dan Arewa ya zama shugaban kasa ba, dan kudu suka sani.