Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa yana Allahbwadai da hare-haren da suka faru tsakanin yarbawa da Hausawa a Shasha jihar Oyo.
Ya bayyana hakane a yayin ziyarar ta’aziyyar da yaje ta rasuwar Tsohon Gwamnan Legas, Lateef Jakande.
Osinbajo yace, Shasha ya kasance waja hada kan al’ummar Najeriya wanda shekara da shekaru Hausawa na kai kayan Amfani suna cinikayya tsakaninsu ds Yarbawa. Yace idan an samu wata matsala, kada a mayar da ita fadan Kabilanci, yace laifi ne wanda kuma ya kamata a bar hukumomi su dauki matakin da ya dace.
Yayi gargadi kan daukar doka a hannu.
We must never take the law into our own hands, if we do we will be promoting chaos, and a breakdown of law and order, and all of us especially the most vulnerable amongst us, will be at risk. I urge all community leaders to work together to preserve the brotherly co-existence that our people from different parts of the country have enjoyed in Shasha market for several decades.
I commend the governor for his swift and decisive action and all the law enforcement agencies for their prompt intervention.