fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Rikon sakainar kashin da manyan Arewa Musulmai suka yi wa yankin ya haifar da Almajirai>>Kukah

Babban Limamin Cocin Katolika, Rabaren Hassan Kukah ya bayyana cewa irin rikon sakainar kashin da manyan Arewa Musulmai suka yi wa yankin ya haifar da almajirai dake gararamba a yankin.

 

 

Kuka ya ce tun farko wannan tsari na karantar da yara ya samu asaline daga kalmar Muhajirun, kuma da shine aka tsara wannan karantarwa tun a abaya, saidai daga baya an gurbata tsarin ta yadda maimakon a yi nasara ci baya aka samu.

 

 

Ya shaida cewa lallai lokaci yayi da za a yi watsi da wannan tsari na Almajirci, kowani da yayi karatu a gaban iyayen sa, sannan ya shiga makarantar Boko.

 

 

” Koda yake fadin haka da gwamnoni suka yi kamar burma wa kai wuka  ne, domin kowa ya sani cewa tsarin almajirci ya dade ana amfani da shi wajen cin wa kai buri na siyasa da tattalin arziki.

 

 

Babban Limami Kukah ya kara da yin fashin baki game da yadda tsarin karatun Almajirci in da ya ke cewa ba ayi wa wadannan yara adalci a lokutta da yawa ba.

 

Karanta wannan  Hakika munyi babban rashi, cewar shugaba Muhammadu Buhari bayan rasuwar Muhammad Barkindo

 

“A kan barsu suna watangaririya a garuruwa dukundukun ba tare da an basu wani kula ba. Sannan kuma ba a yi musu wani shiri ba na koda sun kammala karatun su za su za a sama musu abin yi ko kuma shiri na yadda za su ci gaba a rayuwa da malaman su.

 

 

A dalilin annobar Korona, gwamnonin yankin Arewa 19 suka amince a maida kowani almajiri jihar sa ta asali. Wasu gwamnonin sun amince ada wannan shawara wasu kuma sun ce wannan tsari na maida almajirai jihohin su na asali kamar tauye nusu hakki ne da doka ta basu na iya zama a kowacce jiha a matsayin su na ‘yan Najeriya.

 

 

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya soki wannan tsarin neman ilmi na Almajirci, yadda iyaye ke fatali da yara kakana da sunan neman ilimin addini. El-Rufai ya ce wannan tsari bai yi nasara a kasa Najeriya ba kuma bai haifar wa yankin Arewa mutunci a idanun mutane duniya ba.

Premiumtimeshausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.