Tauraron dan wasan kasar Poland dake taka leda a kungiyar zakarun gasar Bundesliga ta Bayern Munich, Lewandowski ya cika burinsa na konawa Barca a wannan kakar.
Inda gwanin kasuwar kwallon kafa Fabrizio Romano ya bayyana cewa Barcelona ta amince ta saya dan wasan a farashin yuro miliyan 50.
Kwantirakin shekara guda ne ya ragewa Lewandowski a Bayern Munich kuma a kwanakin baya ya fadawa cewa shi Barcelona yake so ya koma.
Kuma yanzu ya cika burin nasa domin kwanan nan Barca zata wuff dashi.