A karshe dai bayan anta fama dashi da kai kawo Robert Mugabe ya yarda ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar Zimbabuwe bayan da ya kwashe shekaru 37 yana mulkin kasar, shugaban majalisar kasar Jacob Mudenda ne ya bayyana haka a gurin zaman da majalisar tayi na yunkurin tsige Mugaben amma kamin a fara sai Mudenda yace Mugaben ya yarda ya sauka daga mulki.