Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha ya roqi babbar kotun tarayya dake Abuja cewa ta barshi yaje kasar waje neman lafiya.
Lauyansa Daniel Alumun ne ya bayyana hakan yayin ake sauraron shari’ar a gaban alkali Iyang Ekwo inda ake zarginsa da satar kudin gwambati lokacin dayake gwamna.
Lauyan nasa ya bayyana hakan ne bayan kotun kira karan nasa wanda EFCC ta kai, amma sai dai hukumar EFCC bata hallaci kotun ba.
Saboda haka kotun tace sai ranar shida ga watan yuli zata saurari korafin Okorocha na cewa ta bar shi yaje kasar waje ya dawo kafin 7 ga watan nuwamba, wanda za’a cigaba da sauraron shari’ar tasa.