fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Ronald Koeman ya tilastawa Suarez yin atisayi shi kadai

Luiz Suarez yana tattaunawa da Barcelona domin su soke mai kwantirakin shi wanda zai kare nan da 2021 bayan ya samu nasara sosai a shekaru shida da yayi a kungiyar. Manema Labarai na Marca sun bayyana cewa Suarez ya amince zai koma Juventus da albashi yuro miliyan tara wanda kuma hakan zai bashi damar yin wasa tare da Cristiano Ronaldo.

Kocin Barcelona Koeman ya gayawa Suarez cewa yayi atisayin shi daban yayin da yake shirin komawa Juventus kuma rahotanni da dama sun bayyana cewa dan wasan yana yin atisayi tare da Vidal da kuma wani kocin wanda ba Koeman ba. Dan wasan Uruguay din ya saka wani hoto a shfin shi na Instagram yayin da yake atisayi da Barcelona kuma ya rubuta babban dan wasa a jikin hoton wanda hakan yake nuna cewa har yanzu shi dan wasan Barcelona ne.
Albashin da Suarez ya amince da shi na yuro miliyan tara a kasar Italiyan zai sa ya ringa daukar albashi kasa da wanda yake dauka a Barcelona amma sai dai dan wasan zai samu karin wasu kudaden musamman ta fannin hotuna. Dan wasan mai shekaru 33 shine dan wasa na uku a cikin jerin yan wasan da suka fi zira kwalaye masu yawa a tarihin Barcelona duk da cewa shekaru shida kacal yayi a kungiyar.
Amma duk da haka sabon kocin kungiyar Ronald Koeman ya bayyana mai cewa baya cikin tsarin shi na kaka zuwa a tattaunawar da suka cikin minti guda a waya, kuma yanzu dan wasan ya shirya barin kungiyar tare da Vidal wanda shima zai koma Inter bada dadewa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.