Tauraron dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo na neman kungiyar da zai koma a wannan kakar, yayin da yake shirin barin Red Devils.
Sabon kocin kungiyar, Hag Ten nada wani tsarin da yake so yayi amfani dashi wurin horas da kungiyar wanda shi kuma Ronaldo bai gamsu da hakan ba.
Manema labarai na kasar Italiya, La Republicca ne suka ruwaito wannan labarin, inda suka ce dan wasan mai shekaru 37 na neman kungiyar zai koma don bashi da matsugunni a United.