fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Ronaldo ya buga wasa na Dubu 1 a Rayuwarsa: Kadarin cin kwallonsa ya karye: Karanta sauran abubuwan kayatarwa na wasan da Juve ta ci Inter 2-0

Tauraron dan kwallon kafa na kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo ya buga wasanni 1000 a rayuwarsa.

 

Hakan ya tabbatane bayan wasan daya bugawa Juve da ta kara da Inter Milan a daren Ranar Lahadi,wasan da ya kare da sakamakon 2-0 bayan kwallayen Aaron  Ramsey da Dybala suka ciwa kungiyar.

 

Wani abin kayatarwa da wannan mataki da Ronaldo ya kai shine, wasanshi na farko a kungiyarshi ta Sporting da Inter Milan suka kara.

 

Wannan nasarar na nufin Juventus ta hau saman teburin Serie A da maki 63, inda ta baiwa Ta Kasanta, Lazio tazarar kaki 1, sai Kuma Inter Milan dake ta 3.

 

An tashi wasan Ronaldo be ci kwallo ko da guda daya ba wanda hakan ke nufin cewa kadarin Ronaldon na jera wasanni 11 yana cin kwallo a kowanne ya karye.

 

Wani abin daukar hankali a wannan wasa shine yanda aka buga wasan babu ‘yan kallo, dalilin haka kuwa shine dokar da kasar ta Italiya ta saka na hana buga wasa da ‘yan kallo saboda cutar Coronavirus har zuwa 3 ga watan Aprilu.

Saidai wani abin daya kara daukar hankali kan Ronaldo a wasan shine, yanda bayan sauka daga Bas din data kaisu filin wasan, duk da cewa babu ‘yan kallo da suka saba tarbarsu da sowa, ya kalli wajan ‘yan da magoya bayan suka saba tsayuwa inda ya daga hannu sannan yawa Kyamara murmushi.

 

Hakanan kuma a cikin filin wasan ma, Ronaldo ya kuma daga hannu sama yana tafiwa kujeru duk da cewa babu ‘yan Kallo akansu.

https://twitter.com/b3naldo7/status/1236749936911253505?s=19

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.