Tauraron dan wasan gaba na kungiyar Manchester United, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa ba zai halacci atisayi yau a saboda wasu ‘yan dalilai.
Kuma kungiyar ta amince masa yayin da kuma ta cigaba da cewa ba zata sayar da shi ba duk da cewa ya bukaci hakan idan ya samu dama.
Kuma gwanin kasuwar kwallon kafa, Fabeizio Romano ya bayyana cewa Chelsea ta taya shi a farashin yuro miliyan 15.