(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ronaldo ne ya fara bude wasan da kwallo bayan da aka dawo hutun rabin lokaci inda Verona ta farke kwallon jim kadan sannan kuma ta samu bugun daga kai sai gola.
Kwallon da Ronaldo ya ci a yau itace kwallo ta 15 da yaci a wasanni 10 daya jera yana ciwa Juve kwallo. Ronaldonne dan kwallo na farko da ya jera wasanni 10 yana ci mata kwallaye ba kakkautawa, a bayanshi akawai Trezeguet wanda shi kuma wasanni 9 ne ya jera yana ciwa kungiyar kwallo a shekarar 2005.
A yanzu jimullar kwallayen da Ronaldo ya ci sun kai 723. Kuma ya jera shekaru 11 kenan yana cin kwallaye a kalla 20 a kowace kakar wasa.
Tun bayan da Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Duniya ta Blon d’Or babu wanda ya kai Ronaldo cin kwallaye da yawa a gaba dayan manyan gasar wasannin Turai 5.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole