fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Ronaldo ya taimakawa Juve da ci 1 a wasan da suka yi 1-1 da AC Milan

Tauraron dan kwallon kafar Juventus, Cristiano Ronaldo ya taimakawa kungiyar tashi ta ci kwallo 1 a wasan da suka buga a daren yau da AC Milan wanda ya kare da sakamakon 1-1.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wasan zagayen farko na kusa dana karshe na cin kofin Coppa Italiya an tafi hutun rabin lokaci ba tare sa cin kwallo daga kowane bangare ba.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokacine, Milan ta saka kwallo 1 wadda ta makale. Ana mintin karshe na wasa, Ronaldo ya so ya ci kwallon ban mamaki da watsewa amma bai yi nasara ba.

A nanne na’urar VAR ta baiwa Juve bugun daga kai sai gola wanda Ronaldo ya ci mata. A yanzu Ronaldo na da kwallaye 12 a wasanni 8 daya buga a shwkarar 2020.

Karanta wannan  Kalli rigar Miliyan 469 da wata 'yar Najeriya ta saka data jawo cece-kuce

An dai yi cece-kuce sosai akan bugun daga kai sai me tsaron gidan da aka baiwa Juve.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.