Sunday, June 7
Shadow

Ronaldo zai bar Juventus, Manchester United na son sayanshi

Manchester United suna son siyan manyan zakarun yan wasan kwallon kafa. Kuma suna harin siyan Harry Kane daga kungiyar Tottenham a kasuwar yan wasan kwallon Kafa. An samu labari cewa Cristiano Ronaldo zai bar kungiyar juventus ayayin da kungiyar suke fama da rashin kudi saboda cutar coronavirus tasa an dakatar da wasanni kwallon kafa kuma United nada ra’ayin siyan shi.

Ayayin da Ronaldo ya bar kungiyar madrid ya koma juventus a shekara ta 2018, anyi tunanin cewa itace kwangilar dan wasan portugal din ta karshe. Yan wasan juventus sun yarda cewa zasu yi hakuri da albashin su har na tsawon watannin hudu don su taimaki kungiyar saboda tana cikin wani mawuyacin hali a yanzu.
Messaggero yace Ronaldo zai bar kungiyar juventus in har suka kasa biyan shi abun yake bukata bayan an gama rikicin coronavirus.
Ronaldo yaci kwallaye 21 a wasanni 22 daya buga a gasar Serie A kuma yaci kwallaye biyu a gasar champions league da kuma biyu a gasar coppa Italia.
A kwanakin baya Woodward yayi kokarin dawo da Ronaldo kungiyar United don ya Karawa masoyan su kwarin gwiwa ayayin da sir Alex Ferguson yayi ritaya. Ronaldo yace yana so ya dawo kungiyar daya ci gasar premier lig har sau uku a shekara ta 2006 zuwa shekara ta 2009. Kuma Woodward yace zai fi so ace Ronaldo ne zasu siya akan kane.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *