fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Rundunar ƴansanda a jihar Katsina ta bukaci al’umma da su yi watsi da wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta na zargin karkatar da kayan tallafin abinci da jami’anta ke yi.

Rundunar ƴansanda a jihar Katsina ta bukaci al’umma da su yi watsi da wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta na zargin karkatar da kayan tallafin abinci da jami’anta ke yi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, PPRO, ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya fitar.

Rundunar ƴansandan ta ce faifan bidiyon ba kawai yaudara ba ne, an fitar da shi ne da nufin bata sunan ƴansanda.

“Bayan cikakken bincike, an gano cewa buhunan shinkafar da aka gani a bidiyon a cikin motar ‘yansanda an kama su ne daga hannun wasu ɓatagari.

“Wasu marasa gaskiya sun yi samu fiye da kason su na kayan agajin , shine ƴansanda suka kama suka kuma mayar da su wurin da aka raba.

Karanta wannan  Za a fara gwajin riga-kafin cutar HIV a Afirka ta Kudu

“Saboda haka abinda bidiyon ta nuna ba shi bane gaskiyar lamari kuma yunƙuri ne na kushe kyakkyawan ƙoƙarin jami’an da aka tura wurin don ba da tallafi, ɗaukar matakan tsaro da tabbatar da gudanar da taron lafiya,” in ji ‘yan sanda.

Rundunar ƴansandan ta kuma tabbatar wa jama’a cewa zarge-zargen da aka yi a cikin wannan faifan bidiyo ƙarya ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *