An kashe ‘yan bindiga da dama yayin da jami’an tsaro na hadin gwiwa suka dakile wasu hare-hare a kananan hukumomi uku da ke jihar Neja
Dakile hare-haren ya biyo bayan kiran gaggawa da rundunar ta samu daga mazauna garuruwan, inda nan take suka isa wajen kuma sukai nasara akan yan bindigar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna a ranar Lahadi, 15 ga watan Mayu.
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Monday Bala Kuryas, ya jagoranci tawagar karfafa dabarun tun daga Minna zuwa Sarkin-Pawa, karamar hukumar Munya kuma an dawo da zaman lafiya.