Rundunar sojin Hadarin Daji ta kama kasurgumin dan bindiga, barawon shanaye kuma dan bindiga, Zwanlan Fatim dan shekara 42 a jihar Filato.
Hukumar tayi nasarar kama shine a karamar hukumar Shendam dake jihar Filaton.
Kuma hukumar ta kama wasu ‘yan ta’addan bayan shi duk dai a jihar ta Filato a harin data kai masu mazauninsu.
Rundunar sojin ta kwato makamai a hannayen su wanda suka hada da bindigu da kuma layoyi.

