fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Rundunar sojin Najeriya ta damke wani kasurgumin dan ta’addan ISWAP daya tsere a gidan kurkukun Kuje

Shugaban sojin Najeriya janar Lucky Irabor ya bayyana cewa sunyi nasarar damke daya daga cikin manyan ‘yan ta’addan ISWAP da suka tsere a gidan Kurkukun Kuje.

A ranar biyar ga watan Yuli ne ‘yan ta’addan ISWAP suka kai harin gidan kurkukun na Kuje dake babban birnin tarayya Abuja.

Wanda suka saki mutane da dama da ake tsare dasu a cikin gidan yarin kusan guda 900 amma hukuma tayi nasarar kamo wasu daga cikin su wasu kuma sun koma da kansu.

Janar Irabor ya bayyana cewa sun kama babban dan ta’addan ISWAP din Idris Ojo tare da Ibarhim Jimoh ne a ranar bakwai ga watan Augusta.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.