fbpx
Monday, August 15
Shadow

Rundunar Sojin Najeriya ta kashe ‘yan Boko Haram guda goma ta ceto mutanen da sukayi garkuwa dasu a Borno

Rundunar sojin Najeriya tayi nasarar kashe ‘yan ta’addan Boko Haram guda goma kuma ta ceto mutanen da sukayi garkuwa dasu a Borno.

Wannan lamarin ya faru ne jiya ranar talata bayan da ‘yan Boko Haram din suka kai hari kauyen Titiya dake Borno suka tare hanya.

Inda aka sanar da rundunar sojin kuma ta kawo masu harin kwantan bauna tayi nasarar kashe goma a cikinsu yayin da kuma wasu suka tsere da raunika.

Kuma ta ceto mutanen da sukayi garkuwa dasu tare da motoci biyu inda suka mikawa masu motocin abinsu sukayi tafiyar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.