fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe wasu sojoji da ba a tantance adadinsu ba a Jihar Neja

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja inda suka kashe jami’an tsaro da dama da suka hada da sojoji da ‘yan sanda.

Rahotanni sun ce akalla mutane 43 da suka hada da sojoji 30 da jami’an ‘yan sanda bakwai da fararen hula ne suka mutu a lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki wurin da ake hakar zinare.

Sun kuma yi awon gaba da wasu ‘yan kasar China da dama.

Karanta wannan  Manchester United tasha kashi daci 2-1 a hannun Brighton

Da take tabbatar da harin, rundunar sojin Najeriya a wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce an kuma kashe wasu ‘yan bindiga a yayin harin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.