Rundunar sojin Najeriya tayi nasarar kashe masu garkuwa da mutane uku a kauyen Mbahuwuhe dake karamar hukumar Katsina Ala a jihar Benue.
Kuma hukumar ta kara da cewa a kwanakin da suka gabata tayi nasarar kama wasu mutane hudu dake garkuwa da mutane a jihar.
Bayan kashe mutanen hukumar tayi nasarar ceto wani mutumun da sukayi garkuwa da shi suka rufe masa idanuwa, yayin da yanzu ake jinyarsa sabod bashi ishasshiyar lafiya.