fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Rundunar Sojoji ta karyata cewa ta buga wani rahoton gargadi game da hambarar da gwamnatin Buhari

Daraktan hulda da jama’a na rundunar soja, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu ya karyata labarin da aka danganta masa game da “Hedikwatar tsaro ta gargadi sojoji a kan hambarar da gwamnatin Buhari”.

Nwachukwu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce jaridar da ke cike da munanan karairayi da kage, ta yi ikirarin cewa “Hedikwatar Tsaro ta yi Allah-wadai da kiran da aka yi na sojoji su karbi mulki”.

Ya ce kafar yada labarai ta yanar gizo ta ci gaba da alakanta abin da ya bayyana a matsayin karya ga “Kakakin Sojoji”.

A cewarsa, abin da ya sa wannan rahoto na rashin bin ka’ida da rashin gaskiya ya ke daukar hankalin jama’a shi ne yadda aka dangana labarin karya ga Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya-Janar. Onyema Nwachukwu, Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito.

Kakakin rundunar ya ce, “Masu rubuta labarin dole ne su zama ‘yan jaridu kawai wadanda ba su san cewa kakakin rundunar ba ya magana da hedikwatar tsaro. Sai dai, domin a fayyace da kuma kiyaye bayanan, muna so mu bayyana cewa babu wani lokaci da Daraktan hulda da jama’a na rundunar ya fitar da wata sanarwa kan lamarin. Don haka, tunaninsu ne, wanda ko ta yaya bai fito daga Nwachukwu ba.”

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Shugaban karamar hukumar mahaifar Atiku Abubakar ya koma jam'iyyar NNPP

Nwachukwu ya ce hafsoshi da sojojin Najeriya ba sa bukatar a yi musu gargadi game da hambarar da gwamnatin Buhari, yana mai cewa biyayyarsu ga kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da kuma babban kwamandan sojojin kasar bai taba shiga shakku ba.

“Rundunar Sojin Najeriya shahararriyar cibiya ce ta kasa kuma mai kishin kasa wacce ta mika kanta ga hukumomin farar hula, bayan da ta tsaya tsayin daka wajen kare dimokradiyyar kasa.

“Za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare kundin tsarin mulkin Najeriya da dimokuradiyyar da aka fi sani da ita ta hanyar ba da taimako ga hukumomin farar hula, a duk lokacin da aka bukaci hakan,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.