fbpx
Tuesday, December 1
Shadow

Rundunar ‘Yan sanda reshan jihar Bauchi ta baje kolin wasu mutane 9 da ake zargi da laifin Fashi da makami

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wasu mutane 9 da ake zargi da fashi da makami.

Wata sanarwa da PPRO, DSP Ahmed Wakili ya fitar, ta bayyana cewa, a ranar 18 ga watan Nuwamba, rundunar ‘yan sanda ta samu bayanai daga kauyan Gudum Hausawa  cewa wasu gungun bata garin sun kutsa yankin domin gudanar da mugun halin su.

A cewarsa, rundunar batai wata-wata ba, nan take ta aike da Jami’an ta, inda su kai nasarar cafke mutum 9.

Wadanda ake zargin sun hada da: Ahmed Umar mai shekaru 22, sai Mohammed Danladi mai shekara 20 sai Abdulsalam Ali mai shekaru 22, da Abdulmumni Zakari Ya’u mai shekaru 18.

Sauran sune: Umar Aliyu dan shekara 21 sai Ibrahim Ahmed mai shekaru 21 Ahmed Adamu mai shekara 18; Usman Yunusa mai shekaru 18 da Basiru Sabo mai shekaru 18 duk a jihar Bauchi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *