Rundunar ‘yan sanda ta jihar Enugu ta cafke mutane 23 da ake zargi da hannu a zanga-zangar SARS wanda ya rikide ya zama rikici a cikin jihar sakamakon haka ya haifar da kashe-kashe da lalata dukiyoyin jama’a.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmad AbdurRahman ne ya bayyana hakan a yayin da ya ke gabatar da wadanda ake zargin a Enugu ranar Laraba.
AbdurRahman ya ce rundunar ta kama wadanda ake zargin ne bisa laifuka daban-daban wanda a cewarsa laifukan sun hada da “laifukan makirci, yin taro ba bisa ka’ida ba da tayar da tarzoma, kisan kai, kone-konen mummunar barna, sata, toshe hanyoyi, tunzura jama’a tare da haifar da rabuwar kai.
Rundunar ta gargadi matasa da su kasance masu bin doka da oda don kaucewa fadawa hannun hukuma.
