fbpx
Monday, August 8
Shadow

Rundunar ‘yan sanda ta cafke tallafin Korona da aka karkatar zuwa Kano

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta ce ta gano katan din taliya 1,958 da ake zargin an karkatar da su daga jihar Benuwai.

Taliyar wacce gidauniyar Aliko Dangote ta bayar don rabawa mabukata a jihar Binuwai.

Hakan na kunshe ne ta cikin jawabin Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Habu Sani ya bayyana ga manema labarai a jihar ranar Laraba.

Hakanan Shugaban ‘yan sandan ya bayyana cewa, rundunar ta gano wasu laimukan kamfanin coca cola da darajar su ta kai dubu N150, wadanda lokacin shansu ya gama aiki.
Haka zalika rundunar ta ce ta kama wadanda a ke zargi da aikata laifuffuka daban daban daga 23 ga watan Yuli zuwa 8 ga watan satumba.

Karanta wannan  Hallau rundunar sojin sama ta sake kashe shugaban 'yan ta'addan jihar Katsina tare da tawagarsa

A cewar hukumar, laifukan sun hada da ‘yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane, da Sauran wadanda ake zargin da su ka hada da dillalan kwayoyi mutum 8, ‘yan damfara 28 da‘ yan daba 146.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.