Monday, March 30
Shadow

Rundunar yan sandan jihar Filato sun kame yan kasuwan da suka ki yin biyayya bisa ga umarnin gwamnatin jihar na rufe kasuwanni

A ranar alhamis ne dai rundunar ‘yan sandan Najeriya a garin Jos ta jihar Filato, suka kame‘ yan kasuwar da ke zargin sun saba wa umarnin gwamnati na kin rufe wajan kasuwancin su.

Jaridar Blueprint ta rawaito cewa an aiwatar da kamen ne a kasuwanni da sauran wurare dake Janta Apata.

Gwamna Simon Lalong ne, a ranar Talata ya ba da umarnin rufe kasuwanni,inda ya umarci hukumomin tsaro su fara aiwatar da doka ta hanyar kame duk wanda aka samu yana keta umarnin da gwamnati ta saka.

Sai dai a bayanan da jaridar ta rawaito ta gano cewa ana zargin yan sanda da karbar na goro har Naira 5000 don sakin wasu daga cikin masu laifin.

Lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato, ASP Ubah Ogaba, ya ce “An gargadi Jami’an mu da kar su karbi kudi daga hannun kowane mutum da ake zargi.

“An kuma hure su da kada su aikata wadancan abubuwan, saboda ya sabawa da’a da dokar aikin dan sanda,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *