fbpx
Monday, March 1
Shadow

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wasu mutum 7 bisa laifin satar mota

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta dakume wasu matasa data kama da laifin satar mota kwanaki kadan bayan sakin su daga gidan gyara kan makamancin laifin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, Orlando Ikeokwu, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya a Owerri.

Ikeokwu, ya ce an samu nasarar cafke su ne bayan da rundunar ta samu rahoto daga wasu mazauna dake yankin Aba a jihar. 

An dai zargi Matasan ne da satar mota kirar LEXUS 350 SUV.

Sai dai lokacin da aka tuhumesu da laifin sun Amsa laifinsu.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *