Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta kai wani samame maboyar masu aikata miyagun laifuka a jihar tare da cafke mutum 27 da ake zargi.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar legas (PPRO) CSP Olumuyiwa Adejobi.
A cewarsa Rundunar ta kai sumamen ne domin kakkabe ayyukan bata gari a jihar baki daya.
Wadanda aka kame sun hada da Olajide Kolawole mai shekaru 26, Kehinde Ayoola, 25, Dola Abdullahi, 20, Michael Ogungbade, 19, da 23. Odumosu.
Hakanan Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada tabbacin cewa rundunar zata cigaba da himmatuwa wajan kakkabe ayyukan bata gari a dukkan sassan jihar.