fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Rundunar ‘yan sandan Kano ta cafke wani malami da laifin azabtar da yaro dan shekara 8 da haihuwa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani malamin makaranta, Ma’aruf Muhammad, mai shekaru 24, bisa laifin azabtar da wani yaro Almajiri mai shekaru 8, Muhammad Garba.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce an kama kakar da mahaifin yaron.

Jami’in PPRO ya ce an kai rahoto ga hukumar ne bayan da aka gano yaron yana yawo a wani rami da ke kusa da Kofar Mata Quarters Kano.

Kakakin ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.