
Matakin Gwamnatin Rwanda na haramta zukar tabar Shisha ya janyo cece-kuce tsakanin ‘yan kasar da ma kasashen da ke makwabtanka da ita.Wasu ‘yan kasar na shakku kan cewa gwamnatin ta dauki matakin haramta tabar ne domin kare kudaden shiga da ta ke samu daga kasuwar taba sigari.
Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya ta fitar a kwanan baya ya bayyana cewa hayakin da ake zuka daga tabar Shisha na tsawon sa’a daya, kamar kwatankwacin zukar hayakin taba sigari guda 100 ne.
Rwanda yanzu ta bi sahun makwabciyarta Tanzania da wasu kasashe kamar Saudiya da Pakistan da Jordan da Singapore da suka haramta shan tabar Shisha.
Wasu ‘yan Rwanda dai na ganin idan har za a haramta shan shisha to ya dace a haramta shan taba sigari.
Shan tabar Shisha dai yanzu ya kasance ado musamman ga matasa a kasashen Afirka.
Rwanda kuma ta haramta shigo da tabar da tallarta da kuma sha saboda dalilai na kare lafiya musamman barazanar cutar kansa da huhu.