Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, a hau jirgin kasa kyauta daga ranar Juma’a har zuwa ranar 4 ga watan Janairu.
Gwamnatin tace ta dauki wannan mataki ne dan saukakawa ‘yan Najeriya yawan tafiye-tafiye da ake a karshen shekara.
Fidet Okhiria, shugaban hukumar kula da sufurin jirgin kasa na Najeriya ne ya bayyana haka.
Ya bayyana cewa, za’a karbi tikitin shiga jirgin amma babu maganar biyan kudi.