Wani sabon bincike da gwamnati Trump ke yadawa ya ce yana ganin hasken rana zai iya taimakawa wajen maganin Coronavirus.
Shugaban kimiya a ma’aikatar da ke kula da harkokin ciki gida, Bill Bryan, ya shaida wa maneman labarai a Fadar White House cewa zafin rana na rage wa cutar tasiri a jikin dan Adam.
Ya ce yayin da yanayin zafi ke karuwa da huci ko babu hasken ranar cutar na mutuwa a cikin gaggawa sama da yadda ake tunani.
Sai dai har yanzu wannan bincike ba a bayyana shi karara ga al’umma ba ko danganta shi da misalai ba.
Mataimakin shugaban kasar Mike Pence ya ce bincike zai taimaka wa Amurka wajen tunkarar annobar a lokacin bazara.
Saidai Wannan bincike bai kawar dabkiran Nesa-nesa da juna ba.
Shuganan kasar Amurkar, Donald Trump ya bayyana cewa yana fatan mutane zasu ji dadin Hasken Ranar.
Godiya Allah da ya sauwaka mana