Wani sabon Rahoto da wata kungiyar dake saka ido akan ayyukan ta’addanci ta Duniya ta fitar yace kungiyar ISIS da aka kafa a kasashen Iraqi da Syria, a yanzu hare-haren su yafi yawa a Najeriya.
Kungiyar dake Geneva a kasar Switzerland me suna jihad Analytics ta bayyana cewa, tun daga fara shekarar 2022 hare-haren da kungiyar ISIS ta kai a Najeriya sun fi wanda ta kai a kasashen Iraqi da Syria yawa.
Kungiyar ISWAP itace wakiliyar kungiyar ISIS a yankin Afrika ta yamma kuma itace ke yada manufofin kungiyar ISIS din a Najeriya da kaddamar da hare-hare da sunanta.
Since the beginning of the year, the Islamic State has conducted half of its attacks in #Africa. For the first time in the history of the jihadi group, Iraq is no longer the country where #IS claims the highest number of operations: the group #ISWAP is now more active in Nigeria. pic.twitter.com/ivlV92DQJo
— Jihad Analytics (@Jihad_Analytics) April 8, 2022
Rahoton yace a karin farko tun bayan kafa kungiyar, Najeriya ta zama kasar da tafi kaiwa hare-hare.
Wannan dai manuniyace ga Shuwagabanni da kuma hukumomin tsaron Najeriya kan cewa su tashi tsaye wajan magance matsalar tsaro dan kar abin ya kara kazanta.