Wani bincike da jaridar Vanguard ta yi ya bayyana cewa ba lallai a fara biyan malaman makaranta da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya wa karin albashi ba a shekarar nan ta 2022 da muke ciki.
Hakan kuwa ya bayyana ne saboda karancin kudi da gwamnatin ke fama dashi.
Koda hukumar dake kula da harkar ilimin wadda itace zata aiwatar da wannan karin albashi a aikace, TETFund kudin shigar da ta yi tsammani a shekarar 2021 biliyan 300 ne amma sai ta samu bilin 197.
Shugaba Buhari dai ya kara yawan shekarun ritayar malamai daga 35 zuwa 40 da sauran abubuwan inganta ayyukan malaman.