fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Sai da na bai wa Obasanjo shawara kada ya shiga siyasa>>Abdulsalami

Tsohon shugaban Najeriya a lokacin soji Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana yadda ya bai wa tsohon shugaban Olusegun Obasanjo shawarar kada ya shiga siyasa shiga siyasa, jim kadan bayan ya fito daga gidan yari.

An tsare Obasanjo ne lokacin shugabancin Janar Sani Abacha kuma ya fito bayan Abdlsalami ya zama shugaban kasa.

Bayan nan kuma Abdulsalami ya mika ragamar kasar ga Obasanjo bayan an zabe shi shugaba a 1999.

An ta sukar Abdulsalami kan mika kasar da ya yi ga wanda ya fito daga kai tsaye daga gidan yari.

Karanta wannan  Tekun Legas ya tafi da dalibai hudu da suka je murna bayan sun lashe jarabawar WAEC

A wata tattaunawa da ya yi da Trust TV Abdulsalami ya yi martani ga masu irin wannan tunani, inda yace wata rana Obasanjo ya ziyarce shi, ya kuma gaya masa mutane na son ya tsaya takara.

Abdulsalam ya ce ya ba shi shawara kan cewa ya yi watsi da wadannan kalamai na mutane ya ta fi gida hutawarsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.