fbpx
Monday, August 15
Shadow

Sai da ‘yan Boko Haram sukawa ‘yan gidan yarin Kuje wa’azi na mintuna 15 kamin suka sakesu

Rahotanni na kara bayyana kan yanda aka gudanar da fasa gidan yarin Kuje dake babban birnin tarayya, Abuja.

 

Kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram dai tace itace ta kai harin inda ma har ta fitar da bidiyo.

 

Rahotanni sun bayyana cewa, sai da kungiyar ta shafe kusan awanni 2 tana cin karenta babu babbaka a harin. Membobin kungiyar akalla 300 ne suka kai harin.

 

Daya daga cikin na gidan yarinnne ya bayyanawa kafar FIJ haka.

 

Rahoton yace ‘yan Kungiyar sun rika baiwa membobinsu kudin mota. Majiyar tace a shirye suka kai harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.