Kungiyar kare muradun inyanurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayyanawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa, idan Ana son zaman lafiya a yankin kudu maso gabas sai an saki Nnamdi Kanu.
Sanarwar dake dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Professor George Obiozor, an fitar da itane bayan taron kungiyar na kwana daya da aka yi.
Kungiyar tace sakin Nnamdi Kanu da sauran wasu matasan Inyamurai da ake zargi da aikata laifuka daban-daban shine matakin farko na dawo da zaman lafiya a yankin.
Tun a watan Yuni na shekarar 2021 ne dai Nnamdi Kanu ke tsare a hannun gwamnatin tarayya bayan kamoshi daga kasar Kenya da aka yi.