fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Sai fa kun taimaka mana kun sa hannu mu yaki ‘yan Bindigar nan tare daku>>Ministan ‘yansanda ya gayawa ‘yan Najeriya

Ministan ‘yansandan Najeriya, Muhammad Dingyadi ya roki ‘yan Najeriya da cewa, sai sun bada hadin kai wajan yaki da ‘yan Bindiga.

 

Ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai a ma’aikatarsa dake Abuja.

 

Yacs bincike ya tabbatar da yawancin masu kai hare-hare kan mutane suna nan zaune tare da mutanen da suke kashewa.

 

Yace suna amfani da masu basu bayanan sirri akan yanda mutane ke tafiyar da al’amuransu.

 

Yace sun siyo kayan aiki na zamani amma kuma duk da haka suna bukatar mutane su basu hadin kai ta hanayar samar da bayanan sirri.

Leave a Reply

Your email address will not be published.