Ministan tsaron Najeriya, Bashir Salihi Magashi ya nemi taimakon Allah kan matsalar tsaron dake addabar Najeriya.
Ya bayyana hakane a sakonsa na Easter inda yace sai an taimaka musu da addu’a akan lamarin.
Saidai yace yana baiwa ‘yan Najeriya tabbacin ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajan magance matsalar tsaron kasar.