Danmasani Birnin Gwari a Jihar Kaduna, Zubairu Abdulra’uf, ya ce sama da shekaru biyu ana biyan ‘yan bindiga N400m a matsayin kudin haraji da girbi kafin manoman Birnin-Gwari su samu damar shiga gonakinsu.
Tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Yada Labarai na Jihar Kaduna, ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Kaduna a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni.
Abdulrra’uf ya kara da cewa ayyukan ‘yan bindiga a kan jama’arsa ya gurgunta harkokin tattalin arziki a yankunan karkara gaba daya kuma ya sa tafiye-tafiye a yankin ya yi matukar wahala ko ma ba zai yiwu ba a wasu wuraren.