fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Sai mun tabbatar da cewa Atiku baiyi nasara a jiharsa ba, cewar shugabannin kananun hukomomin jihar Adamawa

Shuwagabannin kananun hukumomin jihar Adamawa na jam’iyyar APC sun bayyana cewa zasu yi iya bakin kokarinsu don kayar da Atiku a zaben shekarar 2023.

Domin sunce lokacin Tinubu ne kuma suna so shi kansa Atiku ya zabi Tinubu da hannunsa domin a shekarar 1999 ya kawo masu Obasanjo sun zaba saboda haka ya kamata ya saka masu.

Sun bayyana hakan ne a wani taron da suka gudanar a babban birnin jihar watau Yola ranar lahadi.

Kuma sun kara da cewa hatta gwamnan jihar Ahmad Fintiri ba zasu zabe shi ba su Sanata Aishatu Ahmad Binani zasu zaba ‘yar takarar jam’iyyar APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published.