Hukumar bada lamuni ta Duniya, IMF ta bayyana cewa, sai nan da shekarar 2029 farashin kayan masarufi zasu sauko kasa.
Tace ta yi hasashen farashin kayan masarufin zai sauko da kaso 15 cikin 100 nan da shekarar ta 2029.
A yanzu dai, Alkaluman kayan masarufi a Najeriya sun kai maki 33.69 kamar yanda hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana.
Tun dai bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ne dai aka shiga tsadar rayuwa wadda har yanzu babu alamar zata kare.
Ko da a jiya, saida Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, zata sake daukar matakai masu tsauri wanda ka iya kara jefa ‘yan Najeriya cikin halin matsi.
Saidai Gwamnatin tace wadannan matakai da take dauka kokarine na tada komadar tattalin arziki.