Iyalan marigayi Sanata Abiola Ajimobi Wanda tsohon gwamnan Oyo ne da ya rasu a jiya,Alhamis sun bayyana cewa sai Ranar Lahadi me zuwa in Allah ya kaimu za’a yi jana’izar marigayin.
Sanarwar wadda aka fitar ta bakin me magana da yawun marigayin, Bolaji Tunji ta bayyana cewa bayan tattaunawa da gwamnatocin Legas da na Oyo, an yanke shawarar sai Allah ya kaimu Lahadi za’a binne gawar mamacin.
Yayi kira ga masu zuwa gaisuwa da kuma wanda zasu halarci jana’izar su tabbatar sun bi dokar NCDC akan dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.