fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Sai surutu ake ban yi aikin komai ba, to gashi sakataren majalisar Dinkin Duniya yace na yi kokari>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wasu ‘yan Najeriya dake ta kashe gwamnatinsa sun ji kunya saboda gashi daga waje an zo an yabashi.

 

Shugaban yace dama idan na gida basu yaba maka ba to na waje zasu yaba maka.

 

Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Femi Adesina wanda yace ziyarar da sakatarenta majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya kawo Najeriya ta sa ya ga karairayin da ake fada akan kasar ba gaskiya bane.

 

Yace Guterres ya bayyanawa shugaba Buhari a ganawar da suka yi cewa, yayi mamakin ganin irin ci gaban da Jihar Borno ke dashi.

Karanta wannan  "Da Zarar An Zabe Ni Na Zama Shugaban Kasa Za A Daina Dauke Wuta A Nijeriya>>Tinubu

 

Sannan kuma Najeriya kasacee dake kan turbar ci gaba a Afrika dama Duniya baki daya.

 

Adesina yace samar da aikin yi da ilimi da kiwon lafiya ga jama’a na da matukar muhimmanci sosai kuma abinda yaga ana yi kenan a Najeriya.

 

Adesina yace shugaba Buhari na shan wannan yabo ne yayin da wani malamin addini ke fitowa yana cea kasar ta lalace gaba daya.

 

Yace malamin addini kamata yayi ya zama me karfafa jama’a ba me karya musu kargin gwiwa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.