fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Saida muka biya kudin fansa miliyan N6.6 ‘>>Iyayen ‘yan mata 26 da gwamnatin jihar Zamfara tace sulhu aka yi da ‘yan bindiga suka sakesu

Lawal Dogara, shugaban kauyen Dan-Aji da ke karamar hukumar Faskari a cikin jihar Katsina, ya ce an biya miiliyan N6.6 don sakin ‘yan matan 26 da aka sace daga kauyen a ranar 13 ga Oktoba.
Dogara yana mayar da martani ne ga ikirarin da gwamnatin jihar Zamfara ta yi cewa ta tabbatar da sakin mutanen ta hanyar tattaunawa kuma ba a biya kudin fansa ba.
An ce an dauke ‘yan matan ne daga gidaje daban-daban na yankin kuma an kubutar da su daga wani daji a jihar Zamfara.
Mai bai wa gwamnatin Zamfara shawara na musamman kan yada labarai da sadarwa, Zailani Bappa ya ce an saki ‘yan matan ne a ranar 6 ga Nuwamba bayan tattaunawa da’ yan bindigar.
Amma da yake magana da manema labarai a ranar Litinin, Dogara ya musanta ikirarin gwamnatin jihar, yana mai cewa sakin wadanda abin ya shafa ya yiwu ne ta hanyar kokarin iyayensu da sauran al’umma.
Dogara ya ce an biya miliyan N6.6 a matsayin kudin fansa don ceto ‘yan matan, ya kara da cewa an mika kudin ga shugabannin al’umma biyu – Abdulkarim Dan Aji da Liman Babangida Dan-Aji – wadanda suka kai kudin ga masu satar bayan sun yi tattaki na tsawon kwanaki uku a daji.
“Gwamna Matawalle bai shiga cikin sakin nasu ba; kokarin iyayen ne kawai da shugabannin al’umma suka tabbatar da sakin wadanda abin ya shafa, “in ji Dogara.
“Ya kamata gwamnan jihar Zamfara ya daina ikirarin hakan, don sakin matanmu, saboda mun biya don sakinsu.”
Hakimin garin ya kuma ce yayin harin da aka kai wa mutanen, an kashe mutane 15 sannan maharan sun lalata gidaje.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Hukumar 'yan sanda ta damke kasurgumin mashekin data dade tana nama a jihar Osun

Leave a Reply

Your email address will not be published.