fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Sakamakon gwajin matar Gwamnan kaduna ya fito

Uwar gidan gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i Hajiya Hadiza Isma El-Rufai, biyo bayan gwajin da akai mata a ranar lahadi a yau sakamakon nata ya fito inda sakamakon nata ya nuna cewa bata kamu da cutar Covid-19 ba.

Tun bayan sanarwar da mai gidan ta ya bayar cewa ya kamu da cutar Coronaviru a ranar asabar, biyo bayan haka sai Uwar gidan nasa itama aka tabbatar da yi mata gwaji domin duba lafiyarta wanda daga bisani ne rahoto ya bayyana bata dauke da cutar.

A ranar litinin ne uwar gidan gwamnan ta bayyana a shafinta na sada zumunci cewa sakamakon gwajin da akai Mata ya nuna bata dauke da cutar.

Bayan bayyanar hakan itama cibiyar kula da cututtuka ta kasa ta bayyana Kara samun sabbin wanda suka kamu da cutar har kusan mutum 20 wanad biyu daga cikin su yan jihar kaduna ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.