fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Sakamakon wasannin Champions League:Juventus 2-1 Ferencvaros, Dinamo 0-4 Barcelona,Dortmund 3-0 Club Brudge, PSG 1-0 RB Leipzig, Lazio 3-1 Zenit,Manchester United 4-1 Instabul Basaksehir

Alvaro Morata yayi nasarar ciwa Juventus kwallo guda ana daf da tashi wasan su da Ferencvaros bayan Ronaldo ya ramawa Juve kwallon da Uzni ya cisu, yayin da itama Barcelona ta lallasa Dinamo Kiev 4-0 ta hannun Dest da Griezmann da kuma Braitwaite wanda yayi nasarar cin kwallaye biyu.

Itama Dortmund tayi nasarar lallasa Club Brudge 3-0 bayan da Haaland yaci mata kwallaye biyu sai Sancho yayi nasarar cin kwallon nesa, yayin da shima Neymar ya taimkawa PSG da penariti ta lallasa RB Leipzig 1-0.

A karshe dai kungiyar Lazio tayi nasarar cin Zenit 3-1 ta hannun Ciro Immobile wanda yaci kwallaye biyu sai Parolo yaci guda, yayin da Bruno Fernandez yaci kwallaye biyu sai Rashford da James suka kara zirawa Manchester United kwallaye biyu ta lallasa Instanbul Basaksehir 4-1.

Duk dai a gasar ta zakarun nahiyar turai yayin da kuma gabadaya kungiyoyin da suka yi nasarar cin wasannin su yanzu sun cancanci buga wasannin karshe na gasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.