fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Sakamakon Zaben Edo: Saida na zubar da hawaye, Adams Oshiomhole

Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa sai da ya zubar da hawaye saboda zaben na jiharsa wanda abokin hamayyarsa, Gwamna Godwin Obaseki ya lashe.

 

Oshiomhole ya bayyana hakane a wani faifan Bidiyo daya bayyana daya bayyana wanda shine karon farko da yayi magana tun bayan fitar sakamakon zaben.

Yace a rayuwa dama mutum yana iya yinsa ne ya barwa Allah sauran, yace da yaga yanda tsaffi ke fitowa, basu gajiya ba suna zabe sai da ya zubar da kwalla.

Karanta wannan  Babu dan arewar da zai zabi Peter Obi, cewar Kwankwaso

 

Yace kuma hakan ya bashi karfin gwiwar mantawa da abinda ya faru a baya dan ci gaba da fafutuka.

 

Oshiomhole ya jawo hankalin ‘yan Najeriya da a ci gaba da ganin ana karfafa Dimokradiyyar kasarnan domin itace dai kasar mu wadda bamu da kamarta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.